Kwankwaso zai koma jam’iyyar ADC ranar Litinin

RMK RMK 554x430 (1)

Ƙungiyar Kwankwasiyya Movement, ta sanar da cewa jagoranta na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kammala shirye-shiryen shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), inda ake sa ran zai yi rijista a ranar Litinin, 30 ga Maris, 2026, a Kano.

Sanarwar da kakakin ƙungiyar, Habibu Sale Mohammed, ya sanya wa hannu ta ce za a gudanar da rajistar ne a gidan Kwankwasiyya da ke Miller Road da misalin ƙarfe 12:00 na rana.

A cewar sanarwar, wannan mataki wani ɓangare ne na sabbin tsare-tsaren siyasa da shugabancin ƙungiyar ya yanke domin ciyar da manufofinta gaba a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.

Ƙungiyar ta kuma umarci dukkan mambobinta a faɗin Najeriya da su fara yin rijista da jam’iyyar ADC a matakin unguwa, ƙananan hukumomi da jihohi, tare da shiga cikin ayyukan jam’iyyar domin ƙarfafa ta.

Ta kuma bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga bukatar kare dimokuraɗiyya, inganta shugabanci nagari da kuma cika burin al’umma, ta na mai jaddada cewa ƙungiyar na nan a dunkule kuma za ta ci gaba da fafutukar gina Najeriya mai haɗin kai.

A wani ɓangaren kuma, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya gana da Kwankwaso kwanan nan, yayin da kuma fitattun ‘yan siyasa ciki har da Peter Obi suka ziyarce shi a Kano a lokacin Sallah, lamarin da ya ƙara haifar da hasashe kan sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓe mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here