Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da Majalisar dattijai neman bukatar tabbatar da mutane biyar da aka nada a matsayin manyan daraktocin hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA).
Bukatar na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Janairu 31, kuma shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta a zauren majalisar ranar Laraba.
Wadanda aka nada a cewar Buhari sun hada da: Francis Alabo Ogaree, Babban Darakta a masana’antar sarrafa carbon, ginawa da ababen more rayuwa da sufuri da Dr. Mustapha Lamorde, babban darakta a fannin lafiya, tsaro, muhalli da al’umma.
Sauran sun hada da Mansur Kuliya, Babban Darakta a Asusun Kayayyakin Gas na Midstream da Downstream, Bashir Sadiq, Babban Darakta a Sabis na Gudanarwa da Dokta Zainab Gobir, Babban Darakta, Dokokin Tattalin Arziki da Tsare-tsare.
Buhari ya bukaci a gaggauta tabbatar da sunayen wadanda aka nada, domin basu damar fara aiki.













































