Kotu ta dage shari’ar tsohon gwamnan Jigawa Saminu Turaki

00E1C94B A007 40CE 956E B6E115B73A87
00E1C94B A007 40CE 956E B6E115B73A87

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, ta dage shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Saminu Turaki da wasu mutane 4 bisa zargin almundahana da Naira biliyan 36 zuwa ranar 31 ga Maris, 2022.

Solacebase ta ruwaito cewa Sanata Ibrahim Saminu Turaki da wasu mutane 4 na gurfana a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 32 na almubazzaranci da naira biliyan 36. An dakatar da shari’ar shekaru 14 da suka gabata.

An kuma dage shari’ar da aka tsara tun a ranar 24 da 25 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraren karar zuwa watan Maris saboda gazawar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC wajen sanar da wadanda ake kara na biyu da na uku da na hudu a cikin karar.

Haka kuma hukumar ta roki kotun cewa ba ta shirya yin shari’ar ba.

Duk da haka, Lauyan Saminu Turaki, Barr. Saidu Muhammad Tudun-wada duk da cewa bai ki amincewa da bukatar a dage shari’ar ba amma ya nemi a biya shi Naira 500,000 saboda gaza sanar da shi a cikin lokaci mai kyau domin shirya tunkarar shari’ar.

Da yake yanke hukunci kan karar, alkalin kotun, Mai shari’a Hassan Dikko ya amince da dage karar tare da bayar da umarnin biyan N200,000 ga Lauyan wanda ake kara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here