Osinbajo ya kaddamar da ayyukan raya kasa a Maiduguri

54C73A3A 7B92 48F3 8E56 55F13E034726
54C73A3A 7B92 48F3 8E56 55F13E034726

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Alhamis a Maiduguri ya kaddamar da ayyukan da gwamnatin Borno ta aiwatar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa ayyukan da aka kaddamar sun hada da katafaren gini mai shaguna 78, wadanda aka ware wa masu gudanar da kananan sana’o’i a Maiduguri.

Sauran kuma su ne sabbin rukunin gidajen likitocin da aka gina a kan hanyar filin jirgin sama da ke Maiduguri.

Mataimakin shugaban kasan ya kuma gana da ‘yan kasuwa masu karamin karfi a kasuwar GSM ta Maiduguri.

Osinbajo ya nanata kudirin gwamnatin tarayya na karfafa ‘yan kasuwa da kuma karfafa ci gaban kananan sana’o’i a kasar nan.

NAN ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar ministocin ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari da noma, Amb. Maryam Katagum da Baba Shehuri da kuma wasu ‘yan majalisar dokokin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here