Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya Chris Ngige, na shirin ganawa da kungiyar malaman jami’o’i a yau Litinin.
Taron wanda za a fara da yamma zai samu halartar wakilan gwamnatin tarayya da kuma kungiyar ASUU.
Daraktar yada labarai da hulɗa da jama’a a ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya Patience Onuobia, a cikin sanarwar taron da ta aike wa manema labarai a Litinin ɗin nan, ta ce Ngige ne zai jagoranci taron da kansa.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Ministan Kwadago da Aiki, Dr. Chris Ngige, zai gana da kungiyar malaman jami’o’i a yau da karfe 5 na yamma”.
Solacebase ta ruwaito cewa matakin yajin aiki da ASUU ta tsunduma zuwa yau, ya shiga kwana na 56.
A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, 2022 ASUU ta sanar da yajin aikin gargadi na tsawon mako hudu, biyo bayan gazawar ƙungiyar da kuma gwamnatin tarayya wajen cimma matsaya kan buƙatun malaman jami’o’in.
Wasu daga cikin buƙatun na ASUU sun haɗa da sakin kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i, sake tattaunawa kan yarjejeniyar FGN/ASUU ta shekarar 2009, sakin kuɗaɗen alawus-alawus ga malaman jami’o’i, da vatun tsarin UTAS na biyan albashi da alawus-alawus na malaman jami’o’i.













































