Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da naɗa Usman Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban ma’aikata na jihar wanda kafin naɗin nasa babban sakatare ne a ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar.
Sauran manyan sakatarorin gwamnati da aka naɗa sun haɗa da, Injiniya Muhammad Bello Shehu da Magaji Lawan da Bilyaminu Gambo Zubairu da Mairo Audi Dambatta.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Abba Anwar, ya fitar aka rabawa manema labarai da yammacin yau Litinin inda ya ce, naɗin ya fara aiki ne nan take.
Gwamna Ganduje ya taya waɗanda aka naɗa murna sannan ya yaba musu bisa aiki tukuru da suka gudanar a baya na hidimtawa al’umma.
Ya ƙara da cewa “jajircewarku da sanya kwarewa a cikin aikinku na yau da kullum ne ya kawoku ga matsayin da kuke kai a yanzu”. Inji Ganduje.
” Don haka ku sanya a ranku cewa aiki tukuru ne ya sanya kuka maye gurbin wadansu, don haka lallai idanun mutane yanzu haka a kanku yake, ku yi kokari ku baiwa mara da kunya” a cewar gwamna Ganduje.













































