*Gwamnatin tarayya ta karbo sama da Naira biliyan 53 daga cikin Naira triliyan 5 da biliyan 200 na bashin da take bin Ma’aikatu da hukumominta– Minista*

Ahmed Zainab
Ahmed Zainab

Gwamnatin tarayya ta karbo Naira Biliyan 53 da miliyan 500 daga cikin Naira Tiriliyan 5 biliyan 200 daga Ma’aikatu da Hukumomin ta.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a wajen taron kaddamar da shirin tantance basussuka da kuma bayar da rahoton ayyukan Project lighthouse a Abuja ranar Litinin.

Ta ce ma’aikatar ta na yin amfani da wani yunkuri na tattaro adanannun bayanai domin biyan dimbin basussukan da wasu ma’aikatu ke bin Gwamnatin Tarayya.

Zainab Ahmed ta ce ta hanyar karfafa aikin gwamnati ta samu damar hada manyan basuka na kusan Naira Tiriliyan 5 da doriya wanda suke bin hukumomi da ma’aikatunsu, daga ciki an karbo Naira biliyan 53 da miliyan 500 cikin watanni 12 zuwa18 da suka gabata.

Ta ce Project Lighthouse wani shiri ne wanda ya kunshi yin amfani da ci-gaba na tattara bayanai da dabarun tantancewa don gano wadanda basa biyan haraji sai kafa lamunin harajin su da aika sanarwa ga hukumomin da suka dace don yin ayyukan da suka dace.

Ministar ta kara da cewa alkalumman sun fito ne daga bayanan da aka tattara daga masu bin bashi sama da 5,000 a cikin hukumomi da ma’aikatu guda 10.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here