Rundunar Sojojin saman Najeriya ta sa jirgin shugaban kasa a kasuwa

NAF puts up presidential aircraft for sale invites bidders
NAF puts up presidential aircraft for sale invites bidders

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya ta sa jirgin Falcon 900B a kasuwa domin sayarwa, wanda jirgin na daya daga cikin jiragen da shugaban kasa yake amfani da su.

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya tayi shelar siyar da jirgin ne ta kafar X a yammacin ranar Litinin.

A cewar sanarwar, za’a sayar da jirgin ne bayan amincewar gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da siyar da jirgin saman Falcon 900B mallakin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF).

“A bisa tanadin dokar sayan jirgin sama na shekarar 2007, hukumar ta NAF tana gayyatar duk masu sha’awar siyan wannan jirgi da su zo su gabatar da farashin su.”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here