Yobe: Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 10 a harin ƴan ta’adda

Explosion new
Explosion new

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe, ta tabbatar da mutuwar mutane 10 tare da jikkata wasu da dama a wani hari da ƴan tada ƙayar baya na Boko Haram suka a garin Geidam ranar Laraba.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar ASP Dungus Abdulkarim, ne ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan yau Asabar a Damaturu.

Ya ce maharan da ke tafiya a kan babura sun kuma kai farmaki sashen ma’aikata na makarantar gwamnati da ke yankin.

“A halin yanzu al’amura sun dawo dai-dai kuma jama’a na gudanar da harkokinsu na yau da kullun, yayin da aka tura jami’an tsaro domin yin sintiri da aikin gani da ido domin daƙile sake afuwar irin wannan hari a gaba,” inji shi.

Abdulkarim ya ce, rundunar ta jajanta wa al’ummar Geidam kan harin inda ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani motsi da ba su gane masa ba ga hukumomin tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here