Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce jam’iyyar PDP ba ta nuna wani dan takararta ba a matsayin wanda zai yi takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Idan za a iya tunawa, rahotanni sun ce dattawan jam’iyyar PDP na yankin Arewa sun takaita zabin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ga Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa da kuma Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.
A wata sanarwa da Sule Lamido ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana mamakinsa yayin da hankulan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihohin Arewa ke karkata ga rahotannin kafafen yada labarai na cewa wasu dattawan Arewa na jam’iyyar sun fitar da fitattun mutane biyu da suka cancanta, a masalahar ‘Yan Takarar Shugabancin kasa a jam’iyyar PDP.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP, kuma tsohon ministan harkokin waje, ya bayyana cewa bayan tuntubar shugabannin jam’iyyar a fadin jihohin Arewa 19 da babban birnin tarayya Abuja, batun gabatar da wasu mutane 2 a matsayin wadanda suka fi dacewa su tsaya takarar shugabancin kasa ra’ayi ne kawai na wasu mutane wanda kuma hakan zai yi illa ga Kudurorin Arewacin kasar nan.
Ta cikin sanarwar dai Lamido ya ce ana ci gaba da tattaunawa da duk masu neman tsayawa takara a jam’iyyar da nufin samun daidaito matukar zai yiwu ko kuma a yi aiki da shi wajen ganin an gudanar da babban taron kasa ba tare da wata matsala ba.
“Matsayinmu na dattawan Arewa ba wai kawai ya cutar da Arewa ba ne, har ma yana cutar da ‘yan takarar Arewa.”













































