Zargin ɓatanci: Sheikh Lawan Triumph ya bayyana a gaban Majalisar Shura ta Jihar Kano

WhatsApp Image 2025 10 13 at 16.56.53 750x430

Majalisar Shura ta jihar Kano ta gudanar da zaman sirri a ranar Litinin tare da malamin addinin Musulunci Sheikh Lawan Shu’aibu Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph, domin tattauna zargin yin kalaman da ake ganin sun sabawa darajar Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da kungiyoyin addini guda biyar suka gabatar a kansa.

An gudanar da zaman ne a ofishin hukumar tsaron farin kaya (DSS) da ke Kano, inda aka tattauna kalaman da aka danganta ga malamin a wasu bidiyoyi da suka karade kafafen sada zumunta.

Taron ya samu halartar shugaban majalisar, Wazirin Kano Sa’ad Shehu Gidado, sakataren majalisar Shehu Wada Sagagi, daraktan DSS na jihar da kuma wasu malamai masu mukami da ke cikin kwamiti na musamman da aka ɗora wa alhakin binciken lamarin.

Majalisar ta bayyana cewa takardar ƙorafi daga kungiyoyi biyar na addini ta isa gwamnati a watan Satumbar 2025, inda aka tuhumi malamin da yin bayanai da ke saɓawa martabar Annabi.

An tura ƙarar zuwa majalisar domin gudanar da bincike da kuma bayar da shawarwari ga gwamnati.

Karin labari: Zargin ɓatanci ga Annabi: Majalisar Shura ta Kano ta gayyaci Sheikh Lawan Triumph da masu ƙorafi

Majalisar ta ce daga cikin batutuwa tara da aka kawo, an zaɓi huɗu da ake da hujja a kansu, waɗanda suka haɗa da ikirarin cewa an haifi Annabi da kaciya da kuma kwalli, yana da kwarkwata a kansa, da kuma cewa yana ziyartar gidajen matan aure.

Bidiyon da ke ɗauke da kalaman da ake tuhuma da shi da su an kunna shi, kuma malamin ya tabbatar cewa shi ne ya yi bayanan.

Sai dai ya ce an fassara kalamansa ne ta hanyar da ba daidai ba, domin a cewarsa ya yi bayani ne cewa Annabi bai haifu da kaciya ko da kwalli ba, kuma duk wani abin da Allah ya ba shi yana da kima ta musamman.

Wasu malaman majalisar sun ja hankalinsa kan muhimmancin yin taka-tsantsan wajen magana kan abubuwan da suka shafi Annabi saboda saurin fassara da rikitarwa daga jama’a, musamman a jihar Kano da ke da matuƙar kula da batutuwan addini.

Sheikh Triumph ya ce an cire kalamansa daga asalin ma’anar su, inda ya nemi afuwa ga duk wanda ya ji zafi daga maganganunsa, yana mai cewa ba da nufin raini ya fadi hakan ba, sannan ya jaddada cewa yana kaunar Annabi da bin koyarwarsa.

Majalisar ta ce za ta kammala rahotonta tare da shawarwarin da ta cimma, sannan ta mika wa gwamnatin jihar domin daukar matakin da ya dace.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here