Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i su aiwatar da dokar “ba aiki, ba albashi” ga mambobin ASUU

Dr Tunji Alausa Education Minister

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarni ga shugabannin jami’o’in tarayya da su fara aiwatar da dokar “ba aiki, ba albashi” ga mambobin ƙungiyar malamai ta jami’o’i (ASUU) da ke cikin yajin aikin ƙasa baki ɗaya da ake gudanarwa a yanzu.

Wannan umarni na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai kwanan watan 13 ga Oktoba, 2025, wadda Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa ya sanya wa hannu.

An aika kwafin takardar zuwa ga manyan jami’an gwamnati ciki har da shugaban ma’aikatan tarayya, babban sakatare na ma’aikatar ilimi, shugabannin kwamitocin jami’o’i, shugaban ofishin kasafin kuɗi, akanta janar na tarayya da sakataren zartarwa na hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa (NUC).

Labari mai alaƙa: Gwamnatin tarayya ta ce ta cika dukkan bukatun ASUU, don haka babu hujjar ci gaba da yajin aiki

Ma’aikatar ta bayyana takaici kan ci gaba da yajin aikin ASUU duk da kiraye-kirayen da aka yi na tattaunawa, tare da gargadin cewa gwamnati ba za ta ƙara lamunta duk wani mataki da ya sabawa dokokin ƙwadago na ƙasa ba.

Takardar ta jaddada cewa bisa tanadin dokokin ƙwadago, gwamnati za ta aiwatar da dokar “ba aiki, ba albashi” ga duk wani ma’aikaci da ya gaza yin ayyukansa na hukuma yayin da ake yajin aiki.

Alausa ya umarci dukkan shugabannin jami’o’i da su gudanar da ƙididdigar mambobin ASUU da suka halarci aiki da kuma waɗanda suka ƙi, tare da mika rahoto cikakke cikin kwanaki bakwai.

Ya ce a dakatar da biyan albashi ga duk wani malami da bai gudanar da aikinsa ba yayin yajin aikin, sai dai mambobin ƙungiyoyin malamai masu zaman kansu kamar kungiyar Malaman Jami’a (CONUA) da Ƙungiyar (NAMDA) waɗanda ba su shiga yajin aikin ba, su ci gaba da karɓar hakkokinsu.

Ministan ya umurci hukumar NUC da ta sa ido kan yadda jami’o’in ke aiwatar da umarnin tare da mika rahoton bin doka ga ma’aikatar ilimi cikin mako guda.

ASUU ta fara yajin aiki ne a ranar Litinin 13 ga Oktoba, bayan sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, inda ta ce yajin aikin gargadi ne na makonni biyu saboda kin cika alkawuran da gwamnati ta yi na sabunta yarjejeniyar 2009, sakin albashin da aka rike, samar da kudaden farfado da jami’o’i da kuma dakatar da cin zarafin mambobinta a wasu cibiyoyi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here