Gwamnatin tarayya ta ce ta cika dukkan bukatun ASUU, don haka babu hujjar ci gaba da yajin aiki

Morufu Tunji Alausa 678x430

Gwamnatin tarayya ta bukaci kungiyar malamai ta jami’o’i (ASUU) da ta dakatar da yajin aikin da take gudanarwa, tana mai cewa ta riga ta biya dukkan bukatun da kungiyar ta gabatar tare da mika mata sabuwar tayin yarjejeniya.

Ministan ilimi, Dakta Morufu Tunji Alausa, ya bayyana haka a wani shirin talabijin na Channels a ranar Litinin, inda ya ce gwamnati ta gudanar da tattaunawa da ASUU tun bayan karɓar mukaminsa, don haka babu wani dalili na ci gaba da yajin aikin.

Alausa ya bayyana cewa gwamnati ta biya kashi 50 na kudaden alawus na malamai, tare da ware naira biliyan 683 a cikin kasafin kudin 2025 don gina da gyara dakunan kwana, ɗakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje da tarurruka a jami’o’in tarayya.

Karin labari: Da ɗumi-ɗumi: Ƙungiyar ASUU ta sanar da fara yajin aiki a faɗin ƙasa

Ya ce an kuma tanadi kuɗaɗe domin makarantun likitanci, horas da malamai da kuma tallafin ɗalibai ta hanyar asusun ci gaban ilimi da sauran shirye-shirye na gwamnati.

Sai dai ya zargi shugabannin ASUU da hana rarraba kuɗaɗen bukatun gyaran jami’o’i saboda sun nace cewa a basu cikakken kaso na farko su kaɗai, maimakon a raba tsakanin jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma kwalejojin ilimi.

Game da batun albashin watanni uku da rabi da aka dakatar yayin yajin aikin da ya gabata, Alausa ya ce gwamnati ba za ta biya gaba ɗaya ba, domin yarjejeniyar da aka cimma a baya ta tanadi biyan ɓangare kaɗan na kudaden.

Ministan ya kuma tabbatar wa ɗalibai da iyaye cewa gwamnati ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmad Tinubu tana yin duk mai yiwuwa don ganin ba a katse karatu ba, tare da roƙon ASUU da ta janye yajin aikin domin ci gaba da zaman makaranta.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here