Dan El-Rufai da wasu ‘yan majalisa hudu sun sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun

El Rufais son

Dan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Hon. Bello El-Rufai, ya bar jam’iyya mai mulki ta APC ya koma jam’iyyar ADC.

Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya sanar da sauyin jam’iyyar na El-Rufai a yayin zaman majalisa a ranar Alhamis.

Tajudeen ya ce El-Rufai ya koma ADC tare da wasu ‘yan majalisar wakilai biyu na jam’iyyar PDP daga Jihar Kaduna, Hon. Umar Ajilo da Suleiman Richifa.

Kakakin ya kuma sanar da sauyin jam’iyyar Kamilu Ado, dan majalisa daga Jihar Kano, daga ADC zuwa jam’iyyar NDC.

Ya kuma sanar da sauya shekar Hon. Joshua Obika, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar AMAC/Bwari ta Babban Birnin Tarayya, daga APC zuwa NDC.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), ya ruwaito cewa dukkan yan majalisar da abin ya shafa sun bayyana rikicin cikin gida da rashin tabbas a cikin jam’iyyun da suka fito daga gare su a matsayin dalilin sauyin jam’iyyarsu. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here