Kamfanin rarraba wutar Lantarki a Kano (KEDCO) ya bayyana gaskiya kan batun wutar lantarki a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), bayan rahotannin da suka ce katsewar wutar a asibitin ta jawo mutuwar mutane.
A cikin wata sanarwa da shugaban sashin hulɗa da jama’a na KEDCO, Sani Bala Sani, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa an riga an dawo da wutar a asibitin.
Ya ce katsewar wutar ta samo asali ne daga aikin raba layin wutar asibitin daga wuraren zama na ma’aikata.
KEDCO ta bayyana cewa asibitin da sauran cibiyoyin lafiya na AKTH suna da alaƙa da layin 33kV na Zaria Road, wanda yake da matsayi na farko wajen samun wutar lantarki mai kusan awanni 22 a kullum ƙarƙashin tsarin Band A.
Amma, kamfanin ya ce shugabancin asibitin na son a haɗa gidajen ma’aikata da layin da ake amfani da shi a wajen kula da marasa lafiya, wanda hakan ke kawo matsalolin wuta.
Sanarwar ta ce an yi yunƙurin raba layin fiye da sau ɗaya, amma shugabancin asibitin ya ki amincewa, abin da ya haifar da matsalar da ta jawo katsewar wutar da aka fi tsoron faruwa.
KEDCO ya ce yanzu ya fara aikin raba layin domin tabbatar da ci gaba da samun wuta a asibitin ba tare da katsewa ba.
Haka kuma, kamfanin ya bayyana cewa an dade ba a biya kudin wutar da gidajen ma’aikata na asibitin ke amfani da ita ba, duk da cewa hakan yana shafar ingancin wuta da kuma dorewar ayyukan KEDCO.
A cikin wata wasika da Babban jami’in harkokin Kasuwanci na KEDCO, Muhammad Aminu Dantata, ya aika wa Daraktan kula da Asibitin a ranar 12 ga Agusta 2025, ya sanar da shirin cire wuta daga gidajen ma’aikata saboda rashin cikakken biyan kudin wuta.
Wasikar ta nuna cewa bashin da asibitin ke bin KEDCO ya kai Naira miliyan 949.8 a watan Agustan 2025, tare da karin kudin watan Agusta da ya kai Naira miliyan 108.9 wanda ba a biya gaba ɗaya ba.
An bai wa asibitin kwanakin aiki goma domin biyan bashin, in ba haka ba za a dauki matakin cire wutar.
KEDCO ta jaddada aniyarta na ci gaba da samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba ga AKTH a matsayin babban cibiyar lafiya, tare da bukatar shugabancin asibitin ya ba da haɗin kai wajen aikin raba layin.
Kamfanin ya kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa cibiyoyin lafiya, musamman masu kula da sashin gaggawa da rayuwar mutane, za su ci gaba da kasancewa a sahun farko wajen samun wutar lantarki.













































