Hukumar kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta bayyana hasashen cewa daga Litinin zuwa Laraba za a samu ruwan sama mai hade da hadari a sassa daban-daban na ƙasar.
Wannan na cikin sanarwar da aka fitar ranar Lahadi a Abuja daga hukumar.
A ranar Litinin da safe, hukumar ta yi hasashen hadari mai ɗauke da ruwan sama a jihohin Kaduna, Gombe, Bauchi, Kebbi, Adamawa da Taraba.
Daga rana zuwa dare kuma, ana sa ran ruwan sama tare da hadari a arewacin ƙasa, inda aka gargadi yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu yankunan Adamawa, Taraba da Gombe.
A tsakiyar ƙasa kuwa, hukumar ta bayyana cewa za a samu yanayi mai hadari da ɗan hasken rana da safe, sannan daga baya a sami ruwan sama a jihohin Neja, Kogi, Kwara, Babban Birnin Tarayya da kuma Binuwai.
Labari mai alaƙa: NiMet ta yi hasashen Ruwan sama da iska a fadin ƙasar na tsawon kwana Uku
Haka nan a yankin kudu, hukumar ta yi hasashen yanayi mai gajimare da ruwan sama a jihohin Ekiti, Ondo, Ribas, Akwa Ibom da Kuros Riba.
A ranar Talata, an yi hasashen cewa arewacin ƙasa zai fuskanci yanayi mai gajimare tare da ɗan hasken rana da safe, sannan daga baya a sami hadari da ruwan sama a jihohin Borno, Kaduna, Gombe, Bauchi, Taraba da Adamawa.
Daga rana zuwa dare kuma, jihohin Kano, Jigawa, Yobe, Katsina, Zamfara, Kebbi da Taraba za su fuskanci ruwan sama tare da hadari.
A ranar Laraba, hukumar ta yi hasashen yanayi mai gajimare tare da ɗan hasken rana a arewa da safe, inda za a iya samun ruwan sama a Sokoto da Zamfara.
Daga rana zuwa dare kuwa, za a sami hadari da ruwan sama a Borno, Adamawa, Taraba, Kaduna, Zamfara, Kebbi da Sokoto. A tsakiyar ƙasa kuma, jihohin Binuwai, Kogi, Kwara da Neja za su fuskanci ruwan sama mai yawa daga bisani.
NiMet ta shawarci masu ababen hawa da kada su tuka mota yayin ruwan sama mai yawa.
Ta kuma gargadi manoma da kada su yi amfani da taki ko magungunan feshi kafin ruwan sama domin guje wa asarar amfanin gona.
Haka nan hukumar ta ba da shawarar a cire na’urorin lantarki daga soket, a guji tsayuwa kusa da manyan bishiyoyi, tare da shawarci masu zirga-zirgar jiragen sama su nemi rahoton yanayi na musamman daga filayen jiragen sama.
Hukumar ta bukaci jama’a da su rika bin diddigin rahotannin yanayi daga shafin ta na yanar gizo: www.nimet.gov.ng.
NAN












































