Likitoci a asibitin kashi na birnin Kano na gudanar da tiyata karon farko na sauya kashin kafada ga wata mata.
Hotuna daga asibitin dai sun nuna yadda tawagar likitocin suke gudanar da shirye-shiryen yin wannan aiki.
Kafin yau din dai ba’a taba gudanar da irin wannan aiki a Najeriya ba, inda wasu ke kallon hakan ka iya rage yawan ficewa daga kasar zuwa kasashen waje domin neman lafiya.