Kano: Shugaban Karamar Hukuma yayi murabus

Injiniya Ramat, karamar hukuma, murabus, ungogo
Shugaban karamar hukumar Ungogo a Jihar Kano, Injiniya Abdullahi Garba Ramat yayi murabus.A ranar Talata Ramat ya shaidawa SOLACEBASE cewa ya mika ragamar...

Shugaban karamar hukumar Ungogo a Jihar Kano, Injiniya Abdullahi Garba Ramat yayi murabus.

A ranar Talata Ramat ya shaidawa SOLACEBASE cewa ya mika ragamar shugabancin ga mataimakinsa.

Karanta wannan: Likitoci a Jihar Kano suna tiyatar sauya kashin kafada

Ya ce ya sanar da ajiye mukamin na sa ne a wani shiri na karfafawa al’umma a ranar Litinin, a lokacin da ya kama aiki shekaru 3 da suka wuce ya fara shirin taimakon.

Ya ce murabus din nasa na radin kansa ne domin ya ci gaba da gudanar da wasu ayyuka.

Jaridar SOLACEBASE ta kara rawaito cewa wa’adin shugabannin kananan hukumomin Kano ya kare a wannan watan na Febrairun shekarar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here