Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Kano ta kaddamar da runduna ta musamman guda 60 domin inganta tsaro a makarantu.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da rundunar, Kwamandan NSCDC na jihar, Mista Muhammad Lawal-Falala, ya ce an horas da tawagar musamman yadda za a magance matsalar rashin tsaro, ‘yan fashi, fyade, da sauran ayyukan muggan laifuka.
A cewarsa, mata ba sa daukar batun fyade da wasa; don haka, su ne mafi kyawun rukuni waɗanda za su yi yaƙi da barazanar.
Ya bayyana cewa an fara kaddamar da tawagar matan ne a shekarar 2022 a hedikwatar rundunar ta kasa da Kwamandan Janar, Dakta Ahmed Abubakar-Audi.
“Bayan da aka gudanar da cikakken bincike a fadin kasar, an gano cewa makarantu da dama na cikin mawuyacin hali, wanda hakan ya sa ‘yan ta’adda da ‘yan fashi ke kai musu hari.
“Sakamakon binciken ya nuna cewa yawancin makarantun kasar ba su da tsaro, ko dai na gwamnati ko na zaman kansu,” in ji shi.
Ya ce za a tura tawagar ta musamman a makarantun firamare da sakandire, da kuma manyan makarantu domin tabbatar da ingantaccen yanayin koyo.
Lawal-Falala ya bukaci tawagar da su ci gaba da nuna kwarewa wajen gudanar da ayyukansu.
Ya kuma yabawa Gwamna Abba Kabir-Yusuf na Kano, bisa irin goyon bayan da yake baiwa jihar da samar da yanayi mai kyau da zai samar da zaman lafiya a jihar.












































