Garba Shehu, wanda shine mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasan koma gonar sa domin ya ciga da harkoki kiwo da saurin aiki gona, kwana hudu da barin karagar mulki.
Shehu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis mai taken ‘kwana dari bayan Buhari’.
Sanarwar ta ce Buhari ya zabi ya zauna a Daura ne don ya yi nisa da Abuja don kada ya zaman sa a Abuja yazamo matsala ga sabuwar gwamnati, shi isa ya zabe zama a Daura.
Sanarwar ta ce tsohon Shugaban ya karbi dimbin “baki na musamman” wadanda suka hada da mabiya jam’iyya, kungiyoyin talakawa, manoma, mawaka, ma’aikatan jinya, likitoci, shugabannin addini, shugabannin al’umma da sauran kwararru da dama,Domin taya shi murnar anyi mulki lafiya an kuma gama shi lafiya.










































