An rantsar da Douye Diri a matsayin gwamnan Bayelsa a wa’adi na 2

Duoye Diri, rantsar, gwamnan, bayelsa
Gwamnan jihar Bayelsa Duoye Diri ya sha rantsuwar kama aiki a wa'adin mulkin jihar na biyu. An rantsar da gwamnan ne ranar Laraba da rana a babban filin wasa...

Gwamnan jihar Bayelsa Duoye Diri ya sha rantsuwar kama aiki a wa’adin mulkin jihar na biyu.

An rantsar da gwamnan ne ranar Laraba da rana a babban filin wasa na na Samson Siasia da ke Yenagoa babban birnin jihar.

Gwamna Diri da mataimakinsa Lawrence Ewhrudjakpo, sun sha rantsuwar ne a hannun babbar alƙaliyar jihar, mai shari’a Matilda Ayemieye.

Hukumar INEC ce ta ayyana Duoye Diri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

Karanta wannan: ‘Yan gudun hijirar Sudan na cikin matsanancin hali a Chadi – NRC

Manyan mutane da dama ne suka halarci bikin rantsuwar ciki har da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, da tsoffin shugabannin ƙasa irin su Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan da matarsa Patience Jonathan, da mataimakin shugaban ƙasar Laberiya Jeremiah Koung.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci bikin rantsuwar sun haɗar da gwanonin jihohin Oyo da Filato da Neja da Osun da Edo da Kwara da kuma Gwamnan Adamawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here