Gwamnatin tarayya bata rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ASUU ba-Ministan

ASUU ASUU NEW (1)

Gwamnatin Tarayya ta musanta ikirarin cewa ta kulla yarjejeniya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), inda ta dage cewa takardun da aka bayar shawarwari ne kawai.

Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya ce babu wata yarjejeniya da ta kulla tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).

Alausa ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai kan zanga-zangar ASUU da ke gudana a fadin kasar.

Ya jaddada cewa gwamnatin ba ta da sha’awar “yarjejeniya ta bogi ko da ba za ta dore ba” amma don cimma yarjejeniyar da za a iya aiwatar da ita kuma tana goyon bayan hakan

Ya jaddada cewa zanga-zangar da ASUU ta yi a baya-bayan nan ba za ta rikide zuwa yajin aikin ba, saboda gwamnati ta tsunduma tau-taunawa da kungiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here