Mutane Hudu sun mutu, 10 sun jikkata sakamakon gabara da ta kama a wata mota a jihar Jigawa

Accident 1

Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar fasinjoji hudu sakamakon gobara da ta tashi a cikin wata motar safa, yayin da wasu goma suka jikkata.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, SP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Asabar.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a kusa da makarantar sakandare ta ‘yan mata ta Unity da ke karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Asabar wata motar bus kirar Hummer dauke da fasinjoji 44 ta kama wuta a yayin da take kan hanyarta daga karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi zuwa kauyen Rabadi da ke karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Ya kuma bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga wata katifa da ke daure a bayan motar bas, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutane hudu, yayin da wasu goma kuma aka garzaya da su asibiti sakamakon raunukan da suka samu. Sai dai sauran fasinjojin sun tsallake rijiya da baya.

Tuni dai aka mika gawarwakin fasinjojin da suka mutu ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan da likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Dangane da faruwar lamarin, rundunar ‘yan sandan ta bukaci masu tuka ababen hawa da su guji yin lodin fasinjoji da kayayyaki fiye da kima.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here