Rikici ya barke a APC yayin da Ganduje, da minista suke jayayya kan amincewa da shugabancin jam’iyyar na jiha

Ganduje sad 750x430

Wata takaddama mai tsanani a cikin jam’iyyar APC a jihar Kano ta danno kai, kan yunkurin da shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke yi na kokarin sanya wa’adi na hudu na shugaban jam’iyyar a Kano, Alhaji Abdullahi Abbas wanda wa’adinsa ke dab da karewa nan da kwanaki kadan masu zuwa.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa karamin ministan gidaje da raya birane, Alhaji Yusuf Abdullahi Atta, ya yi gargadi cewa, “duk wani yunkuri na baiwa shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Abbas wata dama ta sake haifar da munanan rikici a jam’iyyar ba zai yi tasiri ba”.

Ministan ya yi wannan barazanar ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ‘yan kwamitin jam’iyyar a Kano ranar Asabar.

Atta ya ce a shekarar 2023 APC ce ta lashe zaben Gwamnan Kano inda Gawuna da Sule Garo suka tsaya a matsayin dan takarar gwamna kuma mataimakinsa, amma abin da ya faru shi ne kalaman rashin nuna ɗa’a ga Allah da Abdullahi Abbas ya yi wanda hakan ya sa aka samu rashin nasara.

Rahotanni sun ce shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Umar Abdullahi Ganduje na da hannu dumu-dumu wajen sake nada Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na jiha a karo na hudu.

Ana zargin Ganduje yana da alaka da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jihar don gurgunta damar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin na neman tikitin takarar gwamna a 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here