Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, ya janye daga takarar Sanatan Kano ta Arewa ya kuma bayyana mara wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin baya a matsayin dan takar yarjejeniya gabanin zaben 2027.
Gwarzo ya sanar da janyewarsa ne bayan wani taro da aka gudanar da sanyin safiyar Laraba a Gidan Gwamnatin Kano.
SolaceBase ta ruwaito cewa Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki na siyasa, ciki har da Sanata Barau, tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakin Gwamna Murtala Sule Garo, Hon. Abba Bichi, Shugaban APC na Jihar Umar Haruna Doguwa da sauran shugabannin jam’iyyar.
Da yake jawabi bayan taron, Gwarzo ya ce babban dalilin da ya sa ya ci gaba da kasancewa a cikin ‘yan takarar shi ne saboda matsin lamba da karfafa gwiwar da magoya bayansa suka yi masa na ya tsaya takara.
Sai dai ya bayyana cewa bayan tattaunawa da taruka da dama da masu ruwa da tsaki a Kano da Abuja, ya yanke shawarar janyewa domin kawo zaman lafiya, hadin kai da tabbatar da nasar APC a duka matakai.
A cewarsa, an yanke shawarar ne domin karfafa jam’iyyar gabanin sauran harkokin siyasa da tabbatar da jituwa tsakanin magoya baya a Kano ta Arewa.
Gwarzo ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da Gwamna Yusuf kan rawar da suka taka wajen ganin tattauna da yin sulhu tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
A nasa jawabin, Sanata Barau ya yaba wa Gwarzo kan abin da ya kira sadaukarwa da ya yi domin amfanin jam’iyyar da al’ummar Kano ta Arewa.
Ya kuma yaba wa Gwamna Yusuf kan jagorancin tsarin yarjejeniya da hada shugabannin jam’iyyar tare.
Barau ya yi alkawarin yin aiki tare da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasar APC a kowane mataki a zaben 2027.












































