Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin daurin shekaru 75 a gidan yari, saboda sace kudaden jama’a masu yawa da suka kai kusan Naira biliyan 33.8.
A hukuncin wanda Alkalin Kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya yanke, ya sami tsohon ministan da laifi kuma ya yanke masa hukunci a dukkan laifuffuka 12 na zamba da wawure kudade da Hukumar dake Yaki da Masu yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da shi a gaban kotun.
Duk da an yanke masa shekaru bakwai a kowanne laifi guda 10, kotun ta daure shi shekaru uku da shekaru biyu a kidayar laifi ta hudu da ta biyar na karar.
Mai Shari’a Omotosho ya ce hukuncin ya kamata ya kasance ba tare da zabin biyan tara ba, sai dai a laifi na hudu inda ya ba da izinin biyan tarar Naira miliyan 10.
Bugu da kari, kotun ta umarci a karbe kuɗaden kasashen waje daban-daban da aka samu a hannun wanda aka yanke wa hukunci, da kuma gidaje hudu masu daraja a Abuja da aka gano suna da alaka da shi.
Idan za a iya tunawa, kotun ta samu tsohon ministan da laifi a zaman ta na a ranar 7 ga Mayu da bai halarci zaman kotun ba.
Mai Shari’a Omotosho ya ce ya gamsu cewa hukumar EFCC ta tabbatar da laifin tsohon ministan ba tare da wata shakka ba.
An same shi da laifi a dukkan laifuffukan da ke cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CR/273/2024.
Mamman ya yi aiki a gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Kotun ta gano cewa ya biya tsabar kudin kudi dala dubu 655,700 (daidai da Naira miliyan 200) wajen siyan filaye a Abuja, ba tare da amfani da bin ka’idar kudi ba.
Haka kuma an same shi da laifin cin amana a kan kudafen da gwamnatin tarayya ta fitar domin ayyukan wutar lantarki na Mambilla da Zungeru.
Kotun ta kuma cewa yawancin kudafen an sace su ne ta hanyar masu musanya kudade (BDCs), wadanda suka mayar da kudin zuwa na kasashen waje sannan suka mika wa wanda ake tuhuma.
“Shaidar da aka gabatar tana da karfi sosai idan aka kwatanta da karancin shaidar kare kai da wanda ake tuhuma ya gabatar.
“Wanda ake tuhuma bai gabatar da wata shaida mai gamsarwa don musanta shaidar da aka gabatar da kara ba,” in ji Mai Shari’a Omotosho.
Alkalin kotun ya nuna takaici da cewa wanda ake tuhuma, a matsayinsa na Ministan Wutar Lantarki, bai damu da barin tarihi mai dorewa ba.
“Maimakon barin tarihi na magance matsalar katsewawar wutar lantarki a kasar, wanda ake tuhuma yana rayuwa cikin jin dadi a kan kashin talakawa.
“Ba abin mamaki ba ne cewa har yau ‘yan Najeriya na cikin duhu,” in ji alkalin.
A halin yanzu dai, wanda ake tuhuma bai halarci zaman da aka same shi da laifi ba, haka zalika bai halarta lokacin da aka yanke masa hukunci ba.
Kotun ta bada warantin kama shi.
Lauya, Mista Mohammed Ahmed, wanda ya sanar da wakiltar wanda aka yanke wa hukunci, ya shaida wa kotun cewa bai san inda yake ba, yana mai cewa kiran da ya yi masa bai tafi ba.
Bayan yanke hukuncin, Mai Shari’a Omotosho ya umarci dukkan hukumomin tsaro da su yi aiki tare da Interpol domin tabbatar da kama wanda aka yanke wa hukunci.
Kotun ta ce za a fara kidaya hukuncin ne daga ranar da za a kama shi.











































