Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya maka majalisar dokokin jihar Kaduna kara a kan zargin da ake masa na salwantar da naira biliyan 432 a gwamnatinsa na shekaru takwas, wanda ya bar jihar da dumbin bashin da ake bin sa.
El-Rufa’i ya kai karar majalisar dokokin jihar a gaban babbar kotun tarayya dake Kaduna ne a ranar Laraba, wanda lauyan tsohon gwamnan, Abdulhakeem Mustapha, babban lauyan Najeriya ya shigar, ya kalubalanci rahoton kwamitin majalisar Kaduna wanda ya tuhumi El-Rufa’i kan zargin almundahana.
A cikin karar El-Rufa’i ya bukaci kotun da ta bayyana rahoton binciken Majalisar a matsayin wanda ba shi da tushe balle makama kasancewar ba a ba shi damar sauraron karar da kwamitin ke yi masa da gwamnatinsa ba.
Karin labari: ‘Yan sanda sun kama mai sana’ar POS kan zargin kawalci ga ‘yan fashi
Wadanda suka shigar da karar sun hada da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da Babban Lauyan Jihar da Kwamishinan Shari’a.
Kafin yanzu dai kwamitin wucin gadi da majalisar dokokin jihar ta kafa domin binciken duk wasu kudade da lamuni da kwangilolin da aka bayar karkashin gwamnatin El-Rufa’i ya mika rahotonsa ga majalisar.
Shugaban kwamitin wucin gadi, Henry Zacharia, ya ce yawancin rancen da aka samu a karkashin gwamnatin El-Rufa’i, ba a yi amfani da su wajen biyan bashin ba, yayin da a wasu lokutan ba a bi ka’idojin da suka dace wajen tabbatar da basussukan ba.
Karin labari: Gwamnatin Kano ta bukaci hukumomin agaji su bayyana matsalar da aka samu
Kakakin Majalisar, Yusuf Liman, ya kuma ce an yi zargin cewa gwamnatin El-Rufa’i ta karkatar da zunzurutun kudi har naira biliyan 423 ta bar jihar da dimbin bashin da ake bin sa.
Saidai mai magana da yawun El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya tabbatar da amincin gwamnatin El-Rufa’i kuma ya yi watsi da shi a matsayin abin kunya dangane da ikirarin da kwamitin ya yi.