‘Yan sanda sun kama mai sana’ar POS kan zargin kawalci ga ‘yan fashi

'Yan sanda, kama, sana'ar, POS, kawalci, 'yan fashi, kaduna, abuja
Rundunar ‘yan sanda a Abuja ta kama wani mai sana'ar POS, mai suna Sunday Musa, wanda aka fi sani da Dan Gwari, wanda ake zargin ya kware wajen samar da masu...

Rundunar ‘yan sanda a Abuja ta kama wani mai sana’ar POS, mai suna Sunday Musa, wanda aka fi sani da Dan Gwari, wanda ake zargin ya kware wajen samar da masu yin lalata da ‘yan fashi a sansaninsu, tare da raba kudi ga iyalansu a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Kwamishinan ‘yan sanda a babban birnin tarayyar Abuja, Benneth Igweh, wanda ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a Abuja ranar Talata, ya ce an kama shi ne a wani samame na hadin gwiwa da jami’an hukumar yaki da masu garkuwa da mutane a Kagarko suka gudanar.

Igweh ya ce wanda ake zargin shi ne kuma babban mai bayar da labarai da kayayyaki ga kungiyoyin ‘yan bindiga a karkashin babban kwamandan wani Ardo, wanda ya ce yana nan a guje.

Karin labari: Gwamnatin Kano ta bukaci hukumomin agaji su bayyana matsalar da aka samu

Ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne mai gudanar da zirga-zirgar ma’aikatan jinya da miyagun kwayoyi da masu lalata bisa bukatar kungiyoyin ‘yan fashin.

“Wanda ake zargin ya kuma amsa cewa shi mai sana’ar POS ne da ake hada kai da shi. Ya yi ikirarin cewa ya zuwa yanzu ya raba sama da Naira miliyan 20 a madadin ‘yan fashin,” in ji CP Igweh.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan, wanda ake zargin ya kara tabbatar da cewa ‘yan fashin karkashin jagorancin Ardo (General Kwamanda) na da mutane sama da 15, dukkansu dauke da bindigogi kirar AK-47.

Karin labari: UNILORIN ta nada sabon mai kula da dakin karatu da kuma daraktan aiyuka na jami’ar

Igweh ya kuma bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan ta kuma kama wata matar aure mai shekaru 41 mai suna Ruqayya Ibrahim, wacce ake zargi da kai kayan abinci da sauran kayan aiki ga ‘yan fashin.

Ya ce wacce ake zargin mazauniyar Sabon-Wuse ce a jihar Neja, ta amsa laifin kai kayan abinci ga daya daga cikin kungiyoyin da ke karkashin kwamandan Shumau.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa, an kama wacce ake zargin ne a dajin Gidan-Dogo a kan hanyarta ta kai wa ‘yan fashin abinci, inda ta ce ta jagoranci ‘yan sandan zuwa gidan Shumau, inda aka kwato shanu 14 da aka sace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here