
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga hukumomin bayar da agaji da su kai rahoton duk wata matsala da aka samu wajen aiwatar da ayyuka a jihar.
Yusuf ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da wani shiri kan yadda ake amfani da kudaden tallafi na kasa da kasa (IDF) yadda ya kamata a ranar Litinin a Kano.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan sa, Alhaji Shehu Sagagi, ya jaddada manufar gwamnatin sa na rashin hakuri da cin hanci da rashawa.
Karin labari: ‘Yan majalisu a Najeriya sun rubuta wasika ga shugaba Tinubu kan sakin Nnamdi Kanu
Gwamnan ya bada tabbacin aniyar gwamnatin sa na tabbatar da bin doka da oda, da kuma gaggauta aiwatar da ayyukan da za su amfani al’ummar jihar.
Ya kuma bukaci hukumomin bayar da agaji da su rika kai rahoto gare shi kai tsaye duk wani laifin da aka samu wajen aiwatar da ayyukan.
Babban akanta janar na jiha, Abdulkadir Abdulsalam, wanda ya shirya taron, ya jaddada muhimmancin amfani da kuma aiwatar da shirin na IDF yadda ya kamata domin cimma nasarar gudanar da ayyuka cikin lokaci.
Karin labari: Ɗalibin Nijar ya rasu a hanyar komawa gida daga Sudan
Ya ce jihar ta saki Naira miliyan 600 a matsayin takwararta ta kudade don sabbin ayyuka, wanda ya nuna bukatar kudi da kuma aiwatar da ingantaccen aiki.
NAN ta rawaito cewa taron ya shafi bangarori daban-daban da suka hada da samar da ruwa, noma, abinci, sauyin yanayi, ilimi, tsaftar muhalli, hanyoyin shiga karkara da kuma ayyukan kiwon lafiya.












































