Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta ce ta kama mutane 198 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi tare da tarwatsa gidajen haramtattun kwayoyi guda 21 a Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Mista Sadiq Muhammad Maigatari ya raba wa manema labarai ranar Talata a Kano.
Ya ce an kama su ne a tsakanin 17 ga watan Janairu zuwa 26 ga watan, a cikin wani shiri na “Operation Hana Maye” (Operation Stop Abuse) da Kwamandan Hukumar Abubakar Idris Ahmad ya kaddamar.
An gudanar da aikin ne da nufin yaki da safarar miyagun kwayoyi da kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar.
Karanta wannan: An Dakatar Da Yar Nijeriya a Masalisar Burtaniya Kan Goyon Bayan Gaza
A cewarsa, daga cikin mutane 198 da aka kama, 177 maza ne, 21 kuma mata ne.
“A cikin mutane 198 da ake zargi, an kama mutane 61 a wani kulob da aka mayar zuwa hadahadar miyagun kwayoyi.
“An kama wadanda ake zargin su 42 ne a makabartar Dan Agundi sannan an tarwatsa gidajen miyagun kwayoyi guda 21 da suka hada da makabartar Sheka da Sheka Obajana domin samar da yanayin tsaro da kuma dakile ayyukan da suka shafi miyagun kwayoyi a jihar.”
Karanta wannan: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi amincewar Majalisa don kafa cibiyar kula da cututtuka
Ya ce rundunar ta samu nasarar kwato wasu haramtattun abubuwa kamar maganin roba na Exol biyar da wiwi da sauran abubuwa masu hadari.
Ya nanata kudurin hukumar na kawar da sha da fataucin miyagun kwayoyi.
“Za mu ci gaba da zage damtse wajen ganowa da kamo masu safarar miyagun kwayoyi, da dakile hanyoyin samar da magunguna, da kuma ba da tallafin da suka dace da kuma gyara ga wadanda shaye-shayen miyagun kwayoyi ya shafa.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi da suka shafi sha da fataucin miyagun kwayoyi ga hukumomin da suka dace domin yin hadakar kawo gyara tare da hukumar.