Ba za mu mika wuya ga tsoratarwar ‘yan ta’adda ba – Tinubu

Bola Tinubu scaled 1 750x430

Shugaba Kasa Bola Tinubu ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da yaki da rashin tsaro da tabbatar da sakin duk wadanda ake rike da su a fadin kasar.

Ya ce Najeriya ba za ta mika wuya ga ‘yan ta’adda ko ‘yan fashin daji ba.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ne ya sanar da matsayar Shugaban kasar a ranar Lahadi a wajen ibada ta musamman ta addinai da dama da aka gudanar a National Christian Centre, Abuja, a matsayin wani bangare na shagalin bikin ranar Demokiradiyya na 2026.

A cikin wata sanarwa daga mai taimaka wa Sakataren a fannin yada labarai, Yomi Odunuga, ya ce Tinubu ya bayyana cewa: “Gwamnatin Najeriya ba za ta mika wuya ga ta’addanci, fashin daji ko kowace irin tsoratarwar masu aikata laifi ba.”

Ya jaddada cewa kare rayuka shi ne babban abin da gwamnati ta fi ba da muhimmanci, inda ya ce harin da aka kai a kwanan nan da kuma satar mutane ya nuna cewa dole ne a ci gaba da karfafa ayyukan hukumomin tsaro.

Tinubu ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin tabbatar da dawowar duk wadanda aka sace lafiya, sannan ya sake tabbatar da cewa ana bai wa jami’an tsaro cikakken tallafi domin kare al’umma da kare cikakken ‘yancin kasar.

“Sakin duk wadanda ake tsare da su na daga cikin abubuwan da gwamnati ta fi ba da muhimmanci akai. Ana ba wa hukumomin tsaro da sauran cibiyoyi tallafin da ake bukata domin kare rayuka, tsare al’umma da kiyaye cikakkiyar ‘yancin Najeriya,” in ji shi.

Tinubu ya ce ya himmatu wajen cika alkawiran da kundin tsarin mulki kuma zai “ninka kokari” wajen rage radadin tattalin arzikin da ‘yan kasa ke fuskanta ta hanyar inganta samar da demokiradiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here