Tsohuwar ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Ogun kuma ‘yar tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo, Farfesa Iyabo Obasanjo, ta fice daga jam’iyyar saboda zargin rashin adalci da rashin girmamawa daga shugabannin jam’iyyar.
Iyabo ta bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ta aike wa Shugaban jam’iyyar na jihar, Cif Yemi Sanusi, mai dauke da kwanan wata 31 ga Mayu, 2026, wadda jaridar Nigerian Tribune ta samo a ranar Litinin.
Farfesa Obasanjo, wadda ta yi aiki a jihar a matsayin tsohuwar Kwamishinan Lafiya a wa’adin farko na tsohon Gwamna Gbenga Daniel, sannan kuma ta kasance Sanata mai wakiltar Ogun ta Tsakiya, ta ce sanar da Sanata Solomon Olamilekan Adeola a matsayin dan takarar maslaha ya sabawa ka’idoji da dokokin jam’iyyar kan yadda yarjejeniyar ta dace ta kasance.
Ta ambaci yadda da farko ta yarda ta bi tsarin yarjejeniyar jam’iyyar, inda ta ce ba a tattauna da ita ba kafin a sanar da Adeola a matsayin dan takarar gwamna.
“Lokacin da na fara neman takarar gwamna a wannan jam’iyyar, na zo na gana da kai, na kuma fada maka cewa zan mutunta tsarin maslaha a jam’iyyar da zarar an yi ta.
“Lokacin da ranar ta zo, duk da an yi wa magoya bayana barazana don hana su shiga wajen, na ci gaba da kasancewa cikin nutsuwa. A wurin ba tare da an yi tattauna da ni a matsayina na ‘yar takara kuma la’akari da jagororin jam’iyyar ta kasa kan yarjejeniya, wanda ke bukatar taruka da duk ‘yan takara don su amince da wanda za a sanar, sannan asanar da dan takara.
“Ba wanda ya yarda da kasancewata a taro, la’akari da cewa ni ce babbar abokiyar hamayyar dan takarar da aka zaba, kuma na zagaya jihar ina tarawa da kwadaitar da magoya bayan APC na matakin kasa,” in ji ta a wasikar












































