Majalisar dattawa ta tabbatar da sunayen mutanen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a matsayin kwamishinonin hukumar kula da wutar lantarki ta kasa NERC da kuma hukumar kidaya ta kasa NPC.
Tabbatar da sunayen mutane hudu na NERC a ranar Laraba a zauren majalisar ya biyo bayan nazari tare da amincewa da kwamitin majalisar dattawan kan harkokin wutar lantarki ya yi.
Shugaban kwamitin Sanata Gabriel Suswam (PDP-Benue) ne ya gabatar da rahoton.
Wadanda aka tabbatar da su a matsayin Kwamishinonin NERC na kasa sun hada da: Dokta Yusuf O. Alli (Arewa Ta Tsakiya), Mista Chidi Ike (Kudu maso Gabas), Mista Nathan Rogers Shatti (Arewa maso Gabas) da Mista Dafe N Akpeneye (Kudu maso Kudu).
Majalisar dattawa ta kuma tabbatar da nadin mutane biyar da Buhari ya nada a matsayin kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa (NPC).
Tabbatar da nasu ya biyo bayan yin la’akari da amincewa da rahoton kwamitin tantance mutane ya gabatar.
Shugaban kwamitin Sanata Ya’u Sahabi (APC-Zamfara) ne ya gabatar da rahoton.
Wadanda aka tabbatar da su a matsayin kwamishinonin NPC sun hada da: Cif Benedict Ukpong Effiong (Akwa-Ibom), Mrs Gloria Fateya Izonfo (Bayelsa), Mr Kupuchi Patricia Ori Iyanya (Benue), Dr Haluru Bala (Kebbi) da Dr.Eyitayo Oyekunle Oyetunji (Oyo). .













































