ASUU: Biyan Malaman jami’o’i rabin albashi ba doka ba ne – SERAP

SERAP Buhari
SERAP Buhari

Kungiyar tabbatar da adalci, gaskiya da raba daidan tattalin Arziki ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umarci Ministan Kwadago Chris Ngige da Akanta Janar Sylva Okolieaboh da su gaggauta maido da kudaden da ake cire daga albashin mambobin kungiyar Malaman Jami’o’i na watan Oktoba 2022.”

Kungiyar ta SERAP ta bayyana hakane a matsayin martani, inda ta kuma bukaci shugaban kasa da ya umarci Ngige da Okolieaboh su biya mambobin ASUU cikakken albashi na tsawon lokacin da suka kwashe suna yajin aikin.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da biyan mambobin kungiyar ASUU rabin albashi na watan Oktoba, 2022.

A cikin budaddiyar wasikar mai dauke da kwanan wata 5 ga Nuwamba, 2022 mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan kungiyar Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce: “Biyan rabin albashi ga mambobin kungiyar ASUU haramun ne kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 [Wanda aka yiwa kwaskwarima] da kuma ka’idojin kasa da kasa.”

“Hakkin yajin aikin na nuni da cewa ba a hukunta ma’aikata saboda yajin aiki, Hakanan abubuwan da aka cire sun yi hannun riga da tanadin doka kuma wani nau’i ne na cin zarafi da wulakanta mutum, zalunci dakuma nuna rashin mutuntaka.

“SERAP ta lura cewa kwanan nan ASUU ta dakatar da yajin aikin dasuke na tsawon watanni takwas biyo bayan shigar da su kotun daukaka kara, wanda ya tabbatar da hukuncin da kotun ma’aikata ta yanke a baya.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here