Sha’aban sharada ya taya Shekarau murnar cika shekara 67

R L Ibrahim Shekarau and Shaaban Sharada
R L Ibrahim Shekarau and Shaaban Sharada

Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar ADP Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada OON, ya taya tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau murnar cika shekaru 67 a duniya.

Sakon taya murna ga dan takarar gwamna na ADP na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Abbas Yushau Yusuf ya rabawa manema labarai a Kano.

Sha’aban Sharada ya ce irin gudunmawar da Malam Ibrahim Shekarau ya bayar wajen ci gaban jihar abune da ba za a taba mantawa da shi ba a zukatan al’ummar jihar saboda Gudunmawar da bayarwa a bangaren ilimi.

“Tsarin manufofin sa yayi daidai da irin manufofin jam’iyyarmu, ADP kuma a shirye muke mu inganta ilimi kyauta ga kowa da kowa kalar wanda Malam Ibrahim Shekarau ya yi fice a matsayin daya daga cikin manya-manyan jahohin da suka bayar da gudunmawa sosai a fannin,” in ji sanarwar.

‘’ Honorabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya yi alkawarin dawo da martabar jihar da aka rasa abaya idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kano a zaben watan Maris na 2023

Dan takarar gwamna na ADP ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda jihar ta rasa mutuntaka a idon mutane da dama.

Ya yi amfani da wannan dama a madadin iyalansa, al’ummar mazabar birni, magoya bayan jam’iyyar ADP da dukkan ‘yan kungiyar yakin neman zaben sa suna yi wa Malam Shekarau fatan Allah ya kara masa lafiya, da tsawon rai, da wadata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here