Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce yaki da cin hanci a Najeriya dole ya fara ne daga shugabanni, domin su zama abin koyi ga jama’a da tabbatar da gaskiya da rikon amana.
A yayin wata hira ta kafar Zoom mai taken “Boiling Point Arena” da aka shirya a Abeokuta, Obasanjo ya bayyana cin hanci a matsayin matsala mai tsanani da ta yi wa al’umma katutu.
Ya ce, “Yaki da cin hanci dole ya fara daga kan shugabanni.”
Ya kuma yi kira da watsi da banbance-banbancen kabila, yana mai kiran al’umma da fifita cancanta wajen zaben shugabanni.
Obasanjo ya kara da cewa shugabannin da Allah Ya zaba su ne kawai ke samun nasara a rayuwa.
Ya kuma gargadi shugabannin da suka kai kansu ko aka nada su ta hanyoyin da ba na adalci ba, yana mai misalta irin wadannan shugabbani da shaidanu.
Ya ce, “Cin hanci kamar babbar riga haka yake. Kana gyara wannan hannun, daya hannun na sumbulewa.”