Bayan sauya sheƙar mambobi 3, Ƴan majalisar dokokin Kano na NNPP sun zama 13

kano assembly new 1
kano assembly new 1

Mambobi uku a majalisar dokokin jihar Kano sun sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar NNPP.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa, idan za a iya tunawa ƴan majalisar 10 na jam’iyyar PDP sun koma jam’iyyar NNPP a ranar Juma’a.

Mambobin majalisar sun bayyana matakin nasu ne a wasu wasiƙu daban-daban da suka aike wa shugaban majalisar, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ranar Laraba a Kano.

Babban sakataren yaɗa labarai na majalisar, Malam Uba Abdullahi, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce shugaban majalisar bayan karɓar wasikar a hukumance ya taya su murna tare da yi musu fatan alheri.

Ƴan majalisar uku dai sun haɗa da Abdullahi Yaryasa mai wakiltar mazabar Tudun Wada da Muhammad Butu-Butu mai wakiltar Tofa da Rimin-Gado da kuma Kabiru Ismail mai wakiltar mazabar Madobi.

Haka kuma kamfanin na NAN ya ruwaito cewa sauya sheƙar na ranar Laraba ya sanya adadin ƴan majalisar na jam’iyyar NNPP a majalisar dokokin Kano ya ƙaru zuwa 13, kana adadin mambobin APC ya ragu zuwa 27.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here