Hukumar Kare hakkin masu saye da siyarwa ta kasa (FCCPC), ta ce ta rufe asusu na banki 30 na kamfanonin ba da lamuni, wanda suke aiki ba bisa ka’ida ba.
Mista Babatunde Irukera, Mataimakin Shugaban Hukumar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
Irukera ya kuma ce hukumar ta sa Google da Apple Stores su karbo wasu takardun lamuni daga wasu shafuka, inda ya ce akwai wasu matakai da ake bukata domin hakan ta faru.
Ya ce a halin yanzu Hukumar na tana aiki da wasu manyan kamfanoni rancen kudi har guda uku wadanda lamarin ya shafa domin ganin an magance matsalar.












































