Gwamnan Kano ya bada umarnin yin amfani da kudaden kananan hukumomi domin gina titin Kasa

Abba 1
Abba 1

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aza harsashin ginin gadar kasa da zata shafi sassa 3 da zata lakume Naira biliyan 27.

Gadar da aka aza harsashin yin ta a mahadar Dan’agundi, zuwa shataletalen Tal’udu duk a cikin birnin Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, a wuraren da aka aza harsashin ginin, gwamnan ya ce an fara gudanar da ayyukan ne domin rage cunkoson ababen hawa.

Yace gadojin na da burin saukaka tafiye-tafiye da kawata birnin, baya ga hana gurbatar muhalli, a wani yunkuri na samar da ababen more rayuwa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nanata alkawurran da gwamnatin sa ta dauka na samar da ababen more rayuwa a jihar.

Karanta wannan: Gwamna Radda ya dakatar da jami’i bisa zarginsa da sayar da gandun daji

Ya kuma bayyana cewa, kasafin kudin shekarar 2024 da aka riga aka sanya wa hannu, ya ba da fifiko ga manyan ayyuka, inda zai lakume kaso 60 na kasafin.

Ya yi kira ga dan kwangilar da ke gudanar da aikin da ya tabbatar da kammala aikin a kan lokaci.

Ya kuma yi karin haske kan yadda ake samun kudaden gudanar da ayyukan yana mai cewa ana samun su ne ta hanyar asusun hadin gwiwa tsakanin jiha da kananan hukumomi.

Ya kuma yi kira ga mutanen da ke amfani da hanyoyin da su yi hakuri kan cinkoson da ayyukan ka iya haifarwa tare da tabbatar da cewa ana shirin samar da wasu hanyoyin da za a bi domin saukaka zirga-zirga.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here