BCPG ta bukaci Tinubu da ya dakatar da shirin kara farashin siminti a 2024

Cement

Kungiyar BCPG, mai kare faduwar gine-gine ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu, da ya dakatar da shirin kara farashin siminti a watan Janirun 2024.

Bukatar hakan na kunshe ne cikin sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Juma’a, mai dauke da sa hannun shugaba da sakatariyar kungiyar Sulaimon Yusuf da Adenike Ayanda.

Sanarwar tace Karin farashin idan ya tabbata zai haifar da wagegen gyibi a bangaren gine-gine.

Karanta wannan: Gwamnan Kano ya bada umarnin yin amfani da kudaden kananan hukumomi domin gina titin Kasa

Kungiyar ta bukaci shugaba Tinubu da ya fifita bukatun ‘yan kasa wajen ganin farshin simintin bai karu ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa kungiyar ta kunshi masu kwararrun masu duba gine-gine da masu tsara garuruwa da kwararrun masu zane.

Sauran sun hadar masu iyakance adadin kayan da za’a yi aikin gini da su, da Injiniyoyi da magina da kuma masu duba rukunin gidaje da sauran su.

Tace akwai bayanan sirri dake nuna cewa akwai shirin da kamfanonin siminti ke yin a Karin kudin a sabuwar shekara ta 2024.

Saboda haka kungiyar ta bukaci shugaba Tinubu da ya gayyaci kamfanonin yin siminti domin su tattauna kan batun Karin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here