Gwamnatin Kano ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin N30bn

Kano demolition
Kano demolition

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke mata kan ruguje wasu shaguna a filin Idi da ke cikin birni.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta umurci gwamnatin jihar Kano da ta biya hadaddiyar kungiyar amintattun masu shagunan Idin Massallacin Naira biliyan 30 a matsayin diyyar rugujewar shagunansu ba bisa ka’ida ba ba tare da bin ka’idojin da doka ta shimfida ba.

Sai dai a wata sanarwa da kwamishinan shari’a na jihar Barr. Haruna Isa Dederi, a ranar Juma’a, ya ce gwamnati za ta yi amfani da ‘yancinta na daukaka kara ga kotun daukaka kara ta soke hukuncin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here