mai magana da yauwn rundunar sojin Isra’ila Daniel Hagari ya tabbatar da cewa dakarun na cikin shirin ko-ta-kwana a kan iyakar arewacin Isra’ila.
A baya-bayan nan dai an yi arangama a kan iyakar arewacin Isra’ila da Lebanon tsakanin kungiyar Hezbollah da sojojin Isra’ila.
A ranar juma’ar nan ne ake sa ran shugaban kungiyar Hezbollah da aka ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci a Birtaniya da Amurka da sauran ƙasashe, zai yi jawabi kan yaƙin Isra’ila da Gaza.
Hagari ya kara da cewa, a ranar Alhamis 02 ga watan nuwambar da muke ciki sun gudanar da wani gagarumin farmaki, inda aka auna wasu gungun ‘yan ta’addar Hezbollah, a matsayin mayar da martani ga wani babban harin da ƙungiyar ta kai wanda ya yi sanadin jikkata fararen hula.
Ya jaddada cewa Isra’ila za ta mayar da martani mai karfi kan duk wani harin da aka kai wa fararen hula, kuma tana ci gaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana a kan iyakar arewacin kasar domin tunkarar duk wani abu daka iya faruwa a cikin kwanaki masu zuwa.