Kotun koli ta sanya ranar yanke hukunci kan karar da Farouk Lawan dake daure, ya shigar gabanta

Faruk Lawan
Faruk Lawan

Kotun koli ta sanya ranar 26 ga watan Junairun shekarar 2024, domin yanke hukunci kan karar da tsohon dan majalisar wakilai Farouk Lawan ya shigar.

Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro ta sanya lokacin ne a ranar Alhamis bayan da lauyoyin wancan bangaren suka kammala gabatar da bayanansu.

Faruk Lawan ya daukaka karar ne yana neman a soke hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke tun a ranar 24 ga watan Fabrairun sheakarar 2022, na a daure shi har tsawon shekaru biyar a gidan yari tare kuma da sallamarsa kan tuhume-tuhume biyu daga cikin tuhume-tuhume uku da ake yi masa na zargin cin hanci da rashawa da gwamnatin tarayya ke yi masa.

Yayin da Lauyan Faruk Lawan, Joseph Daudu (SAN) ya bukaci kotun da ta bada belin, ya ce wanda yake karewa baya cikin koshin lafiya.

Daudu ya ce: “Shi (Lawan) yana da ciwon daji wanda har ya kai mataki na uku,” inda ya ce idan har ya kai mataki na hudu, babu tabbacin zai ci gaba da rayuwa.

Amma, da Daudu ya tabbatar da cewa kotun ba ta son ta koma da baya kan matsayarta, sai ya nemi a janye neman belin, daga nan ne aka shigar da babban karar.

Daudu ya bukaci kotun kolin da ta kyale wanda yake karewa sannan ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka karat a yanke.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here