Majalisun dokokin kasar nan sun amince da Karin sama da Naira tiriliyan biyu na kasafin shekarar 2023

Majalisun tarayyar kasar nan sun amince da karin naira tiriliyan 2 da biliyan 176 na kasafin kudin shekarar 2023 wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika wa majalisar a ranar Talata.

Majalisar dattawan ta amince da kasafin ne a ranar Alhamis bayan amincewa da rahoton kwamitin kasafin kudi, wanda shugaban kasafin kudi na majalisar, Sanata Adeola Olamilekan mai wakiltar santoriyar Ogun ta yamma ya gabatar yayin zaman majalisar.

Shugaba Tinubu, a wata wasika da ya karanta a majalisun biyu, ya bukaci ‘yan majalisar tarayyar da su amince da kudirin, wanda shi ne karo na biyu a cikin wannan shekara bayan an amince da Naira biliyan 819 da miliyan dari 5 don samar da tallafin rage radadi ga talakawan Najeriya.

Shugaban a cikin wasikar, ya ce ya zama wajibi a kara samar da karin matakan jin kai da suka hada da bayar da wani tagomashi ga ma’aikatan gwamnati da sauran tsare-tsare don amfanar masu karamin karfi a cikin al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here