Majalisar Dokokin Kano ta fara shirya dokar koyar da ɗalibai da Hausa

Kano State House of Assembly 700x430

Majalisar dokokin jihar Kano ta gabatar da kudirin doka da ke neman tabbatar da amfani da Harshen arsunan gida musamman Harshen Hausa a matsayin Harshen koyarwa a makarantun jihar.

Kudirin mai taken Dokar tabbatar da koyarwa da Harshen uwa na jihar Kano wanda dan majalisa Musa Kachako daga Takai ya dauki nauyi, na da nufin inganta fahimta da rage yawan gazawa a makarantu tare da kare al’adun Hausawa.

Kachako ya bayyana cewa wannan mataki na bin ƙa’idar ƙasashen duniya ne, inda ƙasashe kamar China, Japan da Indiya suka samu ci gaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar fara koyarwa da Harsunan asali tun daga tushe.

Ya ce amfani da harshen Hausa a matakin farko na ilimi zai sauƙaƙa fahimtar darussa, ya rage yawan faduwa a jarabawa, kuma ya karfafa ɗaurewar ɗalibai da makarantu, tare da inganta haɗin kai a fannin ilimi.

Ya ƙara da cewa samar da tsarin doka kan koyarwa da Harshen uwa zai taimaka wajen gina tubalin ilimi mai ƙarfi da sauƙaƙa fahimtar darussan kimiyya da fasaha ga yara.

Bayan tattaunawa, majalisar ta mika kudirin ga kwamitin ilimi na dindindin domin ci gaba da nazari da bayar da shawarwari.

Haka kuma, dan majalisa Zakariyya Nuhu daga Gabasawa ya gabatar da kudiri na kafa makarantar kimiyyar Noma a mazabarsa, wanda zai taimaka wajen habaka harkar Noma da bunkasa tattalin arzikin yankin.

Majalisar ta kuma karɓi wasiƙa daga gwamnatin jihar mai neman amincewar kafa sabon kwalejin kimiyya da fasaha a karamar hukumar Gaya da kuma hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi.

Kakakin majalisar, Isma’il Falgore, ya tura batutuwan ga kwamiti mai alhakin doka domin daukar matakin da ya dace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here