Daliban Kano a makarantar koyar da aikin lauya sun koka kan jinkirin biyan tallafin karatu bayan tantance su

Abba Kabir Yusuf sad 750x430

Daliban jihar Kano da ke karbar horo a Makarantar koyar da aikin Lauya ta Najeriya sun bayyana damuwarsu kan jinkirin biyan tallafin karatun jihar da suke jira fiye da watanni biyar bayan tantancewa.

A cikin wata buɗaɗɗiyar wasika da suka rubuta a ranar 12 ga Satumba 2025, mai dauke da sa hannun Najeebullah Lawan a madadin takwarorinsa, daliban sun nuna takaicinsu cewa duk da kammala tantancewar da hukumar bada tallafin Karatu ta Jihar Kano ta yi tun watanni da suka gabata, har yanzu babu wani bayani game da tallafin.

Daliban sun ce rashin biyan kudin ya jefa su cikin matsanancin hali wajen biyan kudin karatu, siyan littattafai da kayan karatu, da kuma kula da bukatun yau da kullum.

Sun bayyana cewa wahalhalun kudin littattafai da kayan aiki suna hana su mayar da hankali sosai kan karatu, lamarin da ke iya tasiri a nasarorinsu.

Karin labari: Malamai sun halarci gasar karatun Al-Qur’ani ta Shetty a Kano yayin da waɗanda suka yi nasara suka samu kyautar kuɗi

Saboda haka, sun roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta shiga tsakani domin tabbatar da biyan tallafin karatun cikin lokaci, suna mai jaddada cewa hakan zai rage musu nauyin rayuwa, ya karfafa musu gwiwa kuma ya ba su damar yin fice domin su dawo su yi wa jihar Kano hidima da kwarewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here