Dan takarar APC ya lashe zaben cike gurbin Majalisar Tarayya a Kano

APC Convention

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana dan takarar Jam’iyyar APC, Rabiu Shuaibu, a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbin Dawakin Kudu da Warawa a Majalisar Tarayya.

Jami’in da ya ayyana sakamako, Farfesa Umar Sani, ya ayyana Shuaibu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Ya ce Shuaibu ya samu kuri’u 35,356 inda ya doke Lawal Garba Haruna na APM, wanda ya samu kuri’u 268 da na LP Abubakar Yahaya Muhammad da kuri’u 98.

“An fafata a zaben, Rabiu Shuaibu na APC, bayan cika sharuddan doka, an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma an tabbatar da shi zababbe,” in ji shi.

An gudanar da zaben cike gurbin ne domin cike gurbin da rasuwar Muhammad Danjuma Hassan na NNPP ya bari. NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here