Air Peace Zai Kwaso Daliban Najeriya Da Suka Makale A Sudan Kyauta

1931662734949755594 1
1931662734949755594 1

Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya ce zai kwaso daliban Najeriya da suka makala a kasar Sudan da rikici ya barke kyauta zuwa gida.

Rikicin shugabanci ya kasance a Sudan a baya-bayan nan, har ta kai ga rufe sararin samaniyar kasar.

Akalla daliban Najeriya 5,000 da ke Sudan sun nuna matukar bukatar a dawo da su gida Najeriya, inda wasu daga cikinsu ke kokarin tsallaka iyaka zuwa kasar Habasha, mai makwabtaka da Sudan.

Shugaban kamfanin Ake Peace, llen Onyema ne ya sanar da cewa idan ’yan Najeriya da ke Sudan za su iya tsallaka iyaka zuwa kasashen makwabtakan Sudan, to kamfaninsa zai kwaso su zuwa gida a kyauta.

Ya ce aikin kwaso ’yan Najeriyan ya wuce a bar wa gwamnati ita kadai, saboda bai kamata a yi asarar dan Najeriya ko daya a rikicin na Sudan ba.

Gwamnatin Tarayya dai ta yi alkawarin cewa ranar Talata ma’aikatar harkokin kasashen waje za ta fara kwaso ’yan Najeriyan ta kasar Habasha.

Wata sanarwa da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ta ce Najeriya na aiki da gwamantin kasar Habasha, domin amfani da sararin samaniyarta wajen kwashe ’yan Najeriya da suka makale a Sudan.

A ranar Asabar kungiyar daliban Najeriya da ke Sudan ta bukace su da taru a wasu wurare uku da ayyana domin kwashe su zuwa Habasha.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here