Gwamnatin Kano Ta Sallami CMD 3, Ta Dakatar Da Likitoci Da Malaman Jinya

Abba Kabir Yusuf 723x430 1
Abba Kabir Yusuf 723x430 1

Babban sakataren Hukumar Kula da Asibitoci (HMB), ta Jihar Kano, Dakta Mansur Nagoda, ya amince da korar manyan jami’an lafiya na wasu asibitoci uku da ke jihar. Asibitocin da abin ya shafa su ne Babban Asibitin Imam Wali, Abubakar Imam Urology Center da kuma asibitin haihuwa na Nuhu Bamalli.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar, Samira Sulaiman ta fitar kuma ta bayyanawa manema labarai a daren ranar Litinin.

An dakatar da duka likitoci da malaman jinya da suka yi aiki a ranar Lahadi Haka nan kuma, Nagoda ya amince da dakatar da duka likitoci da ma’aikatan jinyan da ke aikin yamma na ranar Lahadi, 30 ga Yulin shekarar 2023.

Ya ce wannan mataki ya zama dole domin hukunta ma’aikatan lafiyar saboda sakaci da suke yi da ayyukansu. Ya kara da cewa, sukan bar aikin kula da marasa lafiya da aka kawo asibitocin a hannun daliban da suka zo koyon aiki, maimakon su tsaya su kula da su da kansu.

Ya ce ba za su lamunci zuwa aiki a makare ba, ko barin wurin aiki ba bisa ka’ida ba da wasu ma’aikatan ke yi, inda ya bayyana cewa duk wanda aka kama yana aikata hakan, zai fuskanci hukunci daidai da abinda dokar ma’aikata ta tanada. Daga karshe Nagoda ya kuma yi kira ga sauran asibitocin da su kara kaimi kan ayyukansu, domin hukumar za ta ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da ayyuka domin farfado da fannin lafiya a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here