Shugaba Bola Tinubu ya sauka Benina domin halartar bikin cika shekara 63 da kafa Jamhuriya.
Benin ta samu yancin kai ne daga Faransa a ranar 1 ga watan Agustan 1960, wata biyu kafin Najeriya ta samu nata yancin.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar na cewa cikin tawagar shugaba Tinubu akwai gwamnoni guda shida, waɗanda shugaba Patrice Talon ya gayyata da kansa.
Gwamnonin sun haɗa da Dapo Abiodun na jihar Ogun da Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas da Seyi Makinde na Oyo da AbdulRahman AbdulRasaq na Kwara da Nasir Idris na Kebbi da kuma Mohammed Bago na jihar Neja.